Allah sarki – Kalli video irin Tashin Hankali da jaruman izzar so suka shiga bayan rasuwar Darakta Nura Mustapha waye – Lifestyle News

Rahotanni sun bayyana cewar jaruman izzar so sunshiga wani mummunan yanayi tun bayan samun labarin rasuwar Daraktan shirin Nura Mustapha waye wanda ya rasu da sanyin safiyar yau lahadi 3/7/2022.

Shima sarki Ali Nuhu wanda shine yake taka rawar Alhaji Matawalle acikin Shirin izzar so shine yashiga halin damuwa inda ya wallafa wani hotonsa tareda da darakta Nura Mustapha waye sannan yayi rubutu a kasa kamar haka:

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah ya jarabcemu da babban rashin. Allah yaji kanka ya kyautata makwanci. Allah yasa Annabi ya barki bakuncinka, jiya warhaka muna tare dakai ana raha Allah yaji kanka da rahama.

Ali Nuhu & Nura Mustapha waye

Haka zalika shima jarumi Lawan Ahmad wanda yake taka rawa a matsayin umar Hashim acikin Shirin izzar so shima yashiga tsananin damuwa wanda babban amininsa ne kuma daraktan sa wanda Allah yamai rasuwa.

Haka zalika Aisha Najamu izzar so da Minal Ahmad (Nana izzar so) da khadija yobe (khareema izzar so) da sauran jaruman cikin shirin sunshiga Damuwa inda saukaita wallafa hoton Marigayi Nura Mustapha waye tareda yimasa addu’ar Allah ubangiji yaji kansa da Rahama yasa aljanna makomarsa amin.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

X