Kalli video Yadda wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Shanye Masa Koko – Lifestyle News

Lamarin ya matukar daga hankalin mutane dake wannan garin domin abun akwai rashin imani ace miji ya kashe matarsa har lahira.

\"\"

Matar ta rasa rantane a wani kauyen kadaura dake karamar Hukumar Rafi a jihar Neja bayan mijin nata dan shekara 20 yayi mata dukan kawo wuka wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta har lahira Innalillahi wa’inna raji’un.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, “Wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi matar tasa duka saboda dan sabanin da suka samu a kan koko.

“Nan take ta fadi magashiyyan, aka dauke ta ranga-ranga zuwa Babban Asibitin da ke garin Wushishi inda likitoci suka tabbatar cewa rai ya yi halinsa.”

Hukumar yan sandan dake yankin sun tabbatar da cewar mijin matar yananan a hannun hukuma domin ya girba abinda ya shuka na rashin tausayi da rashin imani.

“An riga an fara bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu,” inji DSP Wasiu Abiodun.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top