Yawan Tsinuwa Da La’anta Ya Taimaka Wajen Lalacewar Safara’u – Lifestyle Nigeria

Sau da yawa mutane ne suke da?a zama silar shigar wasu mutanen halaka, idan mutum yana aikata sabo basa tunanin su fadakar da shi, kullum tunaninsu ya za a yi su muzanta shi, hakan kuma ke sakawa mai aikata laifin ya cigaba abinsa.

Idan ka saurari hirar da BBC-Hausa su ka yi Safara’u Kwana Casa’in a yau za ka tabbatar da haka.

A lokacin da bidiyon tsiraicinta ya bayyana babu irin cin zarafi da kalaman tsinuwa da la’anta da mutane ba su yi mata ba wanda hakan ya zama silar ?ara shigarta cikin mummunar rayuwa.

Mutane suna mantawa wanne hali a gaba za su tsinci kawunansu ko ?a?ansu ko ?an uwansu domin babu wanda ya fi ?arfin Allah Ya jarrabe shi a rayuwa duk nagartarsa da ingancinsa.

Sannan mutanenmu yanzu musamman a social media sun fi za?ewa akan hango laifuffukan wasu alhali su ma idan aka yi bincike Allah ne ka?ai Ya san irin ta?argazar da su ke aikatawa ?oye.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top