A karon Farko Tahir Fagge Yafadi Dalilin Dayasa Yake Rawa a Gidan Gala – Lifestyle Nigeria

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Tahir Fagge yafito ya bayyanawa duniya dalilin dayasa yake zuwa gidan Gala yana rawa.

Jarumin dai yazabi yafito ya bayyanawa duniya ne gaskiyar abinda ya faru sakamakon yadda mutane suketa cece kuce akan yadda aka gansa yafito yana rawa da kananan yara a gidan gala.

Ya bayyana cewar akwai rashin lafiyar datake damunsa wanda likitoci sunbukaci saiya kawo musu kudi kimanin naira dubu dari biyu da sittin 260,000 wanda yasamu cutar shanyewar barin jiki wanda baya iya doguwar tafiya dole saiya zauna ya huta.

Ya Bayyana cewar yaran sunzo hargida sun samesa inda suka rokesa akan yaje wajan koda bazaiyi rawa ba, kuma suja dauki kudi naira dubu dari da sittin 160,000 suka bashi wanda zai rage saura dubu dari 100,000 kudin su cika domin yakoma asibiti ayi masa magani.

Ya bayyana cewar ya halarci gidan Gala inda aka rokesa ya hau saman fulo ya tsaya koda kuwa bazaiyi rawar ba inda suka dauki wata tsohuwar wakarsa suka saka, ya bayyana cewar a wannan rana ya kara samun naira dubu 100,000 harma dawasu kudade dazai iya ciyarda iyalinsa.

Yakara da cewar akwai halin da mutum idan yashiga kowani irin taimako aka kawo masa dolene zai karba, ya bayyana lokacin dayake fama da rashin lafiyar mutanen dasuka taimaka masa sune Dauda kahuta Rarara yabasa dubu ashirin 20,000 Abdulamart maikwashewa yabashi 15,000 saikuma Abubakar Bashir Maishadda yabasa 20,000.

Tahir Fagge ya bayyana cewar duk wanda suke fitowa suna zaginsa taimakon me sukayi masa a rayuwarsa, ya kara da cewar shi baya damuwa da zagin da mutane sukeyi masa.

Ga video

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top