Darasin Da ‘Yan Fim Za Su Dauka Kan Abokin Sana’arsu Tahir Fagge – Lifestyle Nigeria

Daga Imam Indabawa Aliyu;

Labarin Jarumin fim Tahir Fagge da na karanta cewa matsananciyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita wacce ko tafiya ba ya iya yi da kyau ce ta kai shi ga halin da ya sami kansa, ana bukatar 260k da za a yi masa hoton zuciya, amma ya kasa samu wanda hakan ya kai shi da siyar da mutuncinsa “Idan yana da shi ke nan” na zuwa gidajen gala yana hawa kan dandali yana tikar rawa. A haka ne ya sami wannan kudi.

Wannan babban darasi ne ga masu fim da su daina ‘bata tarbiyya a fina-finansu su zamo mutanen kirki domin duniya abar tsoro ce, kuma daidai take da kowa. Amma da zarar an ce su gyara sai ka ji su da mabiyansu suna cewa ai hassada ake musu.

Mu ba mu ce fim haramun ba ne ba mu ce kar mutum ya yi fim ba. Abin da kawai muka ce shi ne a tsaftace harkar a daina yada badala da fasadi ana lalata tarbiyyar al’umma. ‘Yan matansu cikinsu su daina fakewa da fim suna karuwanci. Mazan kuma su daina kawalci tare da lalata da matan da ke son a saka su a fim.

Mutane nawa ne suka yi tashe a fim amma yanzu rayuwarsu ta koma abun tausayi? Yan matan fim na hawa manyan motoci suna rike manyan wayoyi da suke siya ta harkar karuwanci amma ba sa iya taimakon ‘yan fim yan uwansu. Nan haka Jarumi Moda ya kwanta rashin lafiya suka bar shi ba su tsinana masa komai ba. Sai dai wannan ya kai masa lemo da ayaba ko abarba. Wanda a karshe sai fitowa ya yi yana neman taimakon al’umma a karshe ne aka yanke masa kafarsa.

Haka nan kafin Jarumi Sani S.K ya rasu yana rashin lafiya ba su tsinana masa komai ba, shi ma sai fitowa ya yi yana neman taimakon jama’a kan rashin lafiyarsa. Abun kunya ne duk arzikin da yan kannywood ke ikrarin suna da shi amma ake samun yan cikinsu na tagayyara kan kudin da bai kai ya kawo ba.

Scroll to Top