Buhari yayi Allah wadai da Harin da Yan Boko Haram sukakai a Gidan Yarin Kuje – Lifestyle News

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yakai ziyara gidan gyara halin dake kuje domin duba irin barnar da yan Bindiga sukayi a daren jiya talata 5/07/2022.

\"\"

“Rahotanni sun bayyana cewar yan bindigar sunkai harin da Misalin karfe 10:00pm na dare acewar wani wandake tsare acikin gidan yarin.

Wani ganau ya bayyana cewar yan bindigar sunshigo ta asalin kofar shiga kurkukun inda suka fara harbin kowa tareda harbo abubuwan fashe cikin gidan kurkukun domin kubutar da wanda sukazo tseratarwa.

“Kawo yanzu dai an bayyana cewar kimanin yan kurkuku 300 suka tsere wanda har izuwa yanzu babu labarinsu saidai hukumomin tsaro sun bayyana cewar sunata kokari domin ganin ankamo wanda suka tsere daga cikin kurkukun.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta bayyana cewar zatadau babban mataki wajan cigaba da shawo kan matsalar tsaron data addabi kasar baki daya.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top