Innalillahi za’a saka Yankewa Fatima Kafa a Karo Na Biyu – Lifestyle Nigeria

Innalillahi wa’inna raji’un yanzunnan muke samun rahoton cewar za’a sake yankewa Fatima kafa bayan yankewar da akayi mata a farko.

Idan maikaratu bai mantaba dai Fatima ta hadu dawani jarabawa inda daya daga cikin daliban Makarantarsu ya taka mata kafa da mota wanda hakan yayi sanadiyyar dagargajewar kafarta wanda hakan yasa aka yanke mata kafar a garin sokoto.

Wanda tun bayan faruwar wannan lamarin dai fatima take kwance a asibiti inda ake kula da lafiyarta, kwatsam saimuka tashi dawani labari mara dadi gameda da fatima.

Inda ake fadin cewar za’a sake yankewa Fatima kafa, ma’ana kafar da aka yanke da farko itace za’a sake yankewa domin kuwa akwai wata kwayar cuta data sake shiga kafar wanda inba a yankeba rayuwar Fatima zata shiga wani hali.

Yanzu dai haka Fatima tana garin Abuja inda ananne za’a sake yanke wani waje daga jikin kafar nata da aka yanke da farko. Allah ubangiji yabawa Fatima lafiya dama sauran musulmai marasa lafiya Amin.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top