Kalli video dayasa ala cire jaruma Ummi Alaqa daga shirin Alaqa dakuma shirin Dadinkowa Innalillahi – Lifestyle News

Idan mai karatu bai mantaba dai a watannin baya dasuka wuce ancire Ummi Alaqa daga cikin shirin Alaqa wanda take fitowa inda aka maye gurbinta da jaruma Maryam Yahaya wanda hakan yasa mutane sukaita cece kuce akan hakan.

\"\"

Saidai kwatsam a jiyama ranar asabar 1/7/2022, bayan dawowa da cigaba da shirin Dadinkowa anga yadda aka cire jarumar daga cikin shirin Dadinkowa datake fitowa a matsayin sha’a yarinyar Alkali Dikko budurwa Badaru.

Hakan ya kara saka mutane suke tunanin kodai wani abune yafaru da jarumar shiyasa aka daina ganinta acikin shirye shiryen datake fitowa, duk da jarumar ta tashi da farin jini wajan masoya tun fara fitowarta acikin shirin Dadinkowa.

Saidai Tashar TsakarGida ta rawaito cewar tayi tattaki izuwa ofishin Sarki Ali Nuhu dake Nasarawa GRA domin jik tabakinsa gameda da cire wannan jarumar acikin shirinsa maisuna Alaqa na kamfanin FKD production.

Sarki Ali Nuhu ya tabbatar da cewar wani abu jarumar tayi shiyasa yacirera dag cikin shirin ya maye gurbinta da jaruma Maryam Yahaya bawai dan yafison Maryam Yahaya bane, haka zalika Ali Nuhu ya kara tabbatar da cewar hakan shine zai kare martabar film dinsa da martabar jarumar dakuma martabar masana’antar Kannywood shiyasa aka cireta daga shirin gaba daya.

Ya kara bayyana cewar cigaba da fitowa acikin film ka iya zama mata matsala shiyasa ya bata shawara ta rage fitowa acikin fina finai harsai an shawo kan matsalar datake ciki koma taje tayi aure kawai.

Tashar TsakarGida sun bayyana cewar sunso jin ainahin matsalar amman Ali Nuhu bai fadetaba inda ya bayyana cewar baza’aji hakan daga bakinsa ba shima yanada ya’ dan haka bazaiso hakan ta faru da yarsa ba.
Allah ubangiji ya kyauta.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top