wani Dattino Dan Shekaru 65 Ya Gamu da Ajalinsa A Dakin wata Budurwarsa – Lifestyle Nigeria

Labarin ya matukar tayar da hankalin mutane ganin yadda dattijo dan shekara ashirin ya mutu a dakin budurwa wanda hakan ba dacewa bane.

Mun samu wani labari mai ban mamaki daga Jaridar Vanguard cewa wani mutumi mai shekaru 65 a Duniya ya mutu wajen kwanciya da wata Budurwa a wani otel a Ranar Asabar dinnan da ta wuce.

Wannan mutumi mai suna Obi Nwoda ya shiga daki ne da wata Budurwa mai shekara 34 a wani katafaren otel a cikin Garin Awka da ke Jihar Anambra. Yanzu dai an sanar da Jami’an tsaron da ke Yankin wannan magana.

Tuni aka sheka da gawar wannan Mutumi zuwa wani babban asibiti da ke wajen Garin na Awka inda aka iske ya cika. Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda na Jihar Anambra Mohammed Haruna ya tabbatar da faruwar wannan abin al’ajabi.

Budurwar tace Dattijon yana tare da ita ne a lokacin da ya kife. Yanzu haka dai Jami’an tsaro su na rike da wannan mata inda ake gudanar da bincike a asibiti game da yadda ajali ya auko ma Dattijon kwatsam.

Scroll to Top