Wasu Musulmai sunyi jinyar Abokinsu kirista har zuwa lokacin daya Mutu kuma suka binne Gawarsa a garin Jos – Lifestyle News

Wani abun al’ajabi kenan dabai cika faruwaba inda wani matashi maisuna Isaac Adamu kirista ne yasha fama da jinya harzuwa lokacin mutuwarsa abokansa musulmai suke daukar dawainiyar rashin lafiyarsa.

\"\"

Wannan matashi mai suna Isaac Adamu ya mutu a ranar 5 ga watan Yuli bayan fama da rashin lafiya. Mazaunin unguwar Dadin-Kowa ne dake garin Jos jihar Filato.

Tuni aka yi jana’izarsa a makabartar COCIN dake Kangang.

\"\"

Saidai wani darasin dauka a mutuwar Isaac shine lokacin da yake kan jinya, abokansa wadanda yawanci musulmai ne sun kasance tare da shi a koda yaushe sun dinga bada gudummawar kudin jinyarsa a asibiti, haka ma bayan mutuwar sa abokan nasa musulmai sun tallafawa mahaifinsa har aka kammala jana’izarsa.

Tabbas wannan labarin darasine ga rayuwarmu ta yau da kullum, domin yakamata mutane sudinga zabar abokai nagari wanda zasu taimakesu akowani hali suka tsinci kansu.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint.com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top