Wata sabuwa – Saratu Hashimu Tafara Tattaki Daga Jihar Bauchi zuwa Kano Domin Ganin Mawaki Dauda kahuta Rarara – Lifestyle Nigeria

Wani sabon alamari dazamuce hakan anfi ganin maza sunayi tun lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasamu nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2015, wato tattaki.

Matasa da dama sunyi tattaki daga garuruwa daban daban zuwa Abuja domin taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar cin zabe a shekarun baya dasuka wuce.

Anan kuma wata mata maisuna Saratu Hashimu ce ta dauki haramar tattaki tundaga jahar bauchi izuwa jahar kano domin ta hadu da mawakin siyasa Dauda kahuta Rarara sabida irin kaunar datake masa.

Matashiyar ta fara tattakin ne da yammacin yau Laraba, kamar yadda ta wallafa bidiyon fara tattakin nata a shafin ta na Facebook.

Saidai ganin faifan bidiyon matashiyar yajanyo cece kuce inda wasu sukaita mata fatan alkairi wasu kuma sukaita sukanta da maganganu marasa dadi.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Scroll to Top